(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, yunkurin da wasu ke yi na neman sake dawo da rikici a kasar Syria, manufar hakan ita ce karfafa gwiwar ‘yan ta’adda.
Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya saka a cikin shafinsa na twitter, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Zarif ya kakkausar suka kan yadda wasu kasashen ke hankoron sake mayar da rikicin Syria ya koma danye.
Ya ce yin hakan babu abin da zai haifar illa karfafa ‘yan ta’adda, wanda hakan baa bin alhairi ne ga kowa ba, da hakan ya hada har da masu daukar nauyin ‘yan ta’addan.
Zarif ya ce, dole ne kasashen duniya su hada karfi da karfe wajen yaki da ayyukan ta’addanci, domin kuwa baraza ne ga kowa, kuma dole ne kasashen duniya su daina munafuntar kansu wajen kokarin banbanta ‘yan ta’adda tare da kiran wasu na gari da kuma wadanda ba na gari ba., domin kuwa duka aikinsu guda ne shi ne ta’addanci.
/129